Kungiyar Oxfam ta gargadi dakarun Afghanistan

Tambarin kungiyar Oxfam Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Oxfam ta gargadi dakarun Afghanistan

Kungiyar bayar da tallafi ta Burtaniya, wato Oxfam ta gargadi dakarun Afghanistan da su dakatar da cin zarafin bil Adaman da suke yiwa mutane a kasar.

Kungiyar ta ce dakarun suna cin zarafin mutane, abin da hada da kashe-kashe da yin lalata da kananan yara.

A cikin wani rahoto da kungiyar Oxfam ta fitar, ta ce 'yan sandan Afghanistan da dakarunta, sune suka aikata kashi goma cikin dari na kashe-kashen mutane a kasar a cikin shekarar 2010.

Masu kare hakkin bil Adama dai sun bayyana yadda dakarun Afghanistan ke cin zarafin mutane da cewa, ya wuce gona-da-iri.