An saki tsohon shugaban Nijar Tandja Mamadou

Tsohon shugaban Nijar, Tandja Mamadou
Image caption Tsohon shugaban Nijar, Tandja Mamadou

A Jumhuriyar Nijar, yau da safe ne, kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta sallami tsohon shugaban kasar, Malam Tandja Mamadu, wanda aka tsare a kurkuku tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi ma shi a watan Faibrairun bara.

An tsare shi ne dai bisa zargin almundahana da kudaden jamaa.

Tun a makon jiya ne dai, kotun ta so ta sallame shi, amma alkali mai shigar da kara ya ce akwai sauran zarge-zargen almundahana da ake ma shi, saboda haka sharia ba ta kare ba.

Lawyansa, Barrister Sule Umaru ya ce yana sa ran a yau din nan ma tsohon shugaban kasar zai koma cikin iyalinsa.

Iyalai da magoya bayan tsohon shugaban kasar dai sun yi marhabin da hukuncin da kotun ta yanke.