NATO ta kaiwa Libya hari sau 6000

Barnar da wani hari da NATO ta kai Libya ya yi
Image caption NATO ta kai hari sau 6000 a Libya

Kungiyar kawance ta NATO ta ce, ta kai hare-hare 6000 a Libya, tun bayan fara aikinta na soji a kasar daga ranar 31 ga watan Maris.

Kungiyar ta NATO ta bayyana cewa, aikinta a Libya shi ne tabbatar da takunkumin hana sayarwa kasar makamai, da hana zirga-zirgar jiragen sama, da kuma kare fararen hula.

Sai dai bayan makonni NATO na ruwan bama-bamai a Libya, babu wata alamar da ke nuna cewa Kanar Gaddafi na da aniyar sauka daga kan mulki.

Masu sharhi sun bayyana halin da ake ciki a Libya da cewa yana neman shiga tsaka-mai-wuya.