Obama na son a yi gyara a tsarin shige-da-ficen Amurka

Barack Obama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Obama na son rage yawan masu shigowa Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira da a yiwa dokar shige-da-ficen Amurka gyara ta yadda za a rage yawan masu shiga kasar.

A jawabin da ya yi a Texas da ke makwabtaka da kasar Mexico, Mr Obama ya ce shigar bakin haure cikin kasar na kawo koma-baya ga tattakin arzikinta.

Kiyasi dai ya nuna cewa akwai bakin haure a Amurka kimanin mutane miliyan goma sha daya.

Mr Obama ya ce sauye-sauye a tsarin shige-da-ficen zai rage matsalar yawan bakin hauren da ke shiga Amurka ta haramtacciyar hanya.