An kaddamar da kwamitin binciken rikicin zabe a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan ya kaddamar da wani kwamitin binciken musabbabin rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a wasu jihohin Arewacin Najeriya da kuma wanda aka yi kafin zabe a jihar Akwa Ibom dake kudancin kasar.

Kwamitin mai wakilai 22 dake karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Lemu, zai binciko dalilan rikicin da makaman da aka yi amfani da su da irin barnar da aka yi da kuma asarar rayukan da aka yi.

A jiya Shugaban kasar ya bayar da diyar Naira miliyan 5 ga iyalan kowane dan bautar kasar da ya rasa ransa sakamakon rikicin.

Daruruwan mutane ne dai aka bayar da rahoton sun mutu a lokacin da tarzomar da aka yi a wasu jihohin Arewacin kasar, sanna kuma rahotanni sun ce motoci kusan dari 5 ne aka kona a tashin hankalin da aka yi a Akwa Ibom, gabannin zaben.