'Syria ta fasa neman kujera a majalisar dinkin duniya'

Shugaban Syria, Assad Hakkin mallakar hoto AFP

Kasashen duniya sun ce, matsin lambar da suke yiwa Syria, ya sa ta sauya shawarar neman kujera a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya.

Wakilan kasashen duniya a majalisar sun ce hanyar da Syria ta bi wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati, ta hana ta neman kujerar.

Syria dai na shan suka daga kasashen yammacin duniya da na larabawa da kuma na yankin Asia dangane da yadda take musgunawa 'yan adawa.

Wasu jakadun sun ce a yanzu Kuwait ce ta nuna alamar neman kujerar.