Amurka za ta nuna hotunan Bin Laden

Obama lokacin da ya ke taro da jami'an tsaron Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka za ta nuna hotunan Osama

Hukumar leken asirin Amurka ta CIA, ta ce za ta bari mambobin majalisar dokokin kasar, su ga hotunan gawar Osama bin Laden.

Yau kwanaki 11 kenan bayan kashe Bin Laden da dakarun Amurka na musamman suka yi a Pakistan.

Zuwa yanzu dai, mahukuntan Amurka sun ce hotunan na da matukar muni, kuma za su iya haddasa tashe-tashen hankula.

A wani lamarin kuma hukumomin leken asirin Amurkar sun ce Bin Laden ya ajiye wani kundin adana bayanai, wanda aka kwace lokacin da aka kai harin. Har yanzu dai ba a bayyana abin da kundin ya kunsa ba.