Dimeji Bankole ya nemi gafarar majalisa

Shugaban majalisar wakilai ta Nigeria, Dimeji Bankole ya bayyana a gaban majalisar a yau, bayan da a jiya suka nemi da ya gurfana a gabansu domin amsa wasu tambayoyi ko kuma su dakatar da shi.

A jiyan dai yan majalisar sun kwashe sa'o'i suna jiran a bude majalisar domin soma zama, saidai mataimakin Shugaban majalisar ya nemi gafara game da lamarin.

Zama daya ne dai kawai Shugaban ya halarta tun da ta koma daga hutun zabe.