An rantsar da shugaba Museveni na Uganda

Yoweri Museveni
Image caption Yau za a rantsar da Museveni

An rantsar da shugaba Yoweri Museveni na Uganda kan wani sabon wa'adin mulki. Shugabannin Afrika da dama ne suka halarci bikin a Kampala babban birnin kasar.

Bikin ya zo daidai da dawowar jagoran 'yan adawa Kizza Besigye daga kasar Kenya, bayan ya yi jinyar raunukan da dakarun Uganda suka ji masa.

Dr Besigje tare da matarsa na dosar birnin Kampala ne tare da daruruwan magoya bayansa.

Ya yi DAI watsi da sakamon zaben shugaban kasar da aka yi a watan Fabreru.

Wakilin BBC wanda ke wurin ya ce abin tambaya shi ne yadda jami'an tsaro za su maida martani kan tawagar Mr Basyge a daidai lokacin da shugaba Musebbeni ke karbar rantsuwa.