Rahoto kan take hakkin bil adama

Tambarin kungiyar Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil adama Amnesty International, ta ce kasashen larabawa na yunkurin dakatar da boren da mutane ke yi a kasashen, ta hanyar amfani da hanyoyin musayar ra'ayi da muhawara.

Galibi dai jama'a a kasashen larabawa da na gabashin Afirka sun yi amfani da sabbin hanyoyin sadarwar irin su Facebook da Twitter wajen aikewa da sakonni a lokacin da aka gudanar da zanga-zanga a kasashen.

Sai dai a rahoton da ta fitar na shekara-shekara kan kare hakkin bil adama, kungiyar Amnesty International, ta yi gargadi ga kamfanonin sadarwar da su turjewa gwamnatocin da ke son yin amfani da su don hana mutane fadar albarkacin bakinsu.

Kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da cewar shekarar 2011, ba ta kasance wacce ta yi kaurin suna wajen take hakkin bil adama ba.