Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Daukar HIV/AIDs daga uwa zuwa jaririnta

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Yara da dama ne ke kamuwa da cutar HIV/AIDs a sassa daban daban na duniya

A kalla yara dubu dari 370 ne suka kamu da cutar HIV a shekarar 2009 kuma mafi yawa daga cikinsu a cewar hukumar lafiya ta duniya, sun kamu da cutar ne daga iyayensu mata.

Hanyoyin yada cutar daga uwa zuwa jaririnta sun hada da lokacin da uwa take goyon ciki, yayin haihuwa ko kuma ta shayarwa.

Haka kuma hukumar ta bayyana cewa kare yaduwar cutar daga uwa zuwa ga jaririnta abu ne mai yiwuwa, musamman a guraren da ke da ingantaccen harkar kiwon lafiya, sai dai batun ba haka yake ba a kasashen da ba su da karfin tattalin arziki.

Batun samun kariya daga yaduwar cutar HIV ko Sida daga uwa zuwa ga jaririnta na daga cikin manyan batutuwan da Majalisar Dinkin Duniya ta duba a wani zama na musamman da ta yi a shekarar 2001.

Inda kasashen da su ke karkashin Majalisar su ka yi alkawarin rage kamuwa daga cutar da jariran ke yi daga iyayensu mata da kashi 50 cikin dari adaga wancan lokaci zuwa shekarar 2010.

Shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa na wannan makon ya duba batun yaduwar cutar HIV daga uwa zuwa jaririnta.