An kai Suzanne Mubarak asibiti

Suzanne Mubarak
Image caption Suzanne Mubarak

An kwashi uwargidan tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak zuwa wani asibiti bayan da ta yi fama da cutar da ake zargin bugun zuciya ce.

An kwantar da ita a wani asibiti dake Sharm El sheik, wasu 'yan sa'oi bayan da aka bada umarnin tsare ta har na tsawon kwanaki goma sha biyar, kafin a kammala bincike kan zarge zargen aikata zamba cikin aminci da ake yi ma ta.

A ranar alhamis din da ta gabata ne dai Suzane Mubarak, ta amsa tambayoyi daga hukumomin kasar a karo na farko, a daidai lokacin da aka tsawaita tsarewar da ake yiwa maigidanta da makonni biyu.

Mr. Mubarak dan shekaru tamanin, yana fuskatar caje caje, wadanda suka hada da mallakar dukiya ba ta hanyar da ta dace ba.