Yau ake bikin ranar 'yancin matan Nijar

A jamhuriyar Nijar yau ne matan kasar ke gudanar da shagulgulan ranar da gwamnatin kasar ta kebe domin su.

Galibi matan, da gwamnati da abokan arziki kan yi amfani da wannan ranar domin yin nazari a kan halin da rayuwar matan na Nijar ke ciki domin duba matakan shawo kan matsalolin da suke fuskanta.

Bikin na yau na duba irin ci gaban da matan na Nijar suka samu daga 1991 lokacin shirya babban taro na kasa , Conference Nationale da ya bada damar girka dimokaradiyya a kasar, kawo yanzu. Shugaban kasar ta Nijar Alhaji Mahamadu Isufu , da shugaban majalisar dokoki Malam Hama Amadu ,da Praministan na Nijar Briji Rafini duk sun halarci bikin.