An yi mummunar hadarin mota a jihar Yobe

Wani hadarin mota a Najeriya
Image caption Wani hadarin mota a Najeriya

Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya sun nuna cewar kimanin mutane goma sha tara ne suka rasu yayinda wasu suka jikkata sakamakon wani mummunan hadarin motar da ya abku a kauyen Kukar Awo dake kusa da garin Potiskum.

Hadarin dai ya abku ne da misalin karfe sha dayan rana bayan da wata motar safa, "Jigawa Sunrise" wadda ta taso daga Kano makare da fasinjoji kan hanyar ta ta zuwa Maiduguri ta yi taho mu gama da wata motar safar da ta dauko fasinjoji daga Maidugurin zuwa Kano inda bayan sunyi watsi da wasu fasinjojin dake ciki suka kama da wuta.

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a wannan makon dai sun ce, mutane miliyan guda da dubu dari ukku ne ke mutuwa a kowace shekara a duniya, sakamakon hadduran motoci, kuma kimanin miliyan hamsin suna jikkata.