Jami'an Amirka sun gaana da maatan bin Laden

Daya daga cikin maatan Osama bin Laden Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daya daga cikin maatan Osama bin Laden

Amurka ta ce jami'anta sun yi hira da uku daga cikin matan Osama bn Laden a kasar Pakistan.

Matan dai sun tsira ne daga harin da sojojin Amurkan suka kai a kan gidan da Osama bn Laden yake a garin Abbottabad.

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon dai ba za ta bayyana abubuwan da suka tattauna da matan ba, amma akwai rahotannin dake cewar an samu rashin fahimta tsakanin Amurkar da Pakistan game da tattaunawar da matan na Osama bin Laden.