Cutar AIDS na cigaba da yin illa a Kudancin Afrika

Wata mai fama da cutar AIDS
Image caption Wata mai fama da cutar AIDS

Wata kididdiga da hukumar lafiya ta duniya, WHO ta fitar na nuna irin illar da cutar AIDS ko SIDA ta yi wa al'ummar kudancin Afrika.

Tun daga shekarar 1990, an samu raguwa ta yawan shekarun da ake sa ran mutane za su rika yi a duniya, da shekaru tara, a Afrika ta Kudu, da kuma shekaru sha biyu a kasashen Swaziland da Zimbabwe.

A daidai wannan lokaci kuma an samu karuwar shekarun ne a wasu sassa na duniya, ciki har da sauran kasashen Afrika.

Sashen Kudancin Afrika dai shi ne wanda cutar ta AIDS ko SIDA ta fi yi wa illa.