An tsaurara matakan tsaro a Yauri na jihar Kebbi

Wata mai jefa kuria a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata mai jefa kuria a Najeriya

Rahotanni daga garin Yauri na Jihar Kebbi sun ce an tsaurara matakan tsaro a garin, domin hana magoya bayan wani dan takarar majalisar tarrayya karkashin inuwar jam'iyyar PDP yin wata babbar zanga-zanga, domin nuna rashin amincewa da matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na baiwa wata mata takardar shaidar lashe zabe a maimakonsa.

A jiya ne dai a wajen wani bikin gabatar da takardun lashe zaben gwamna da 'yan majalisar jahar, hukumar ta INEC ta mika takardar ga Hajiya Halima Tukur a zaman wadda ta lashe kujerar mazabar majalisar wakillai ta Yauri/Shanga/Ngaski a maimakon Alhaji Garba Umar Uba wanda ya lashe zaben fitar da dan takarar kujerar a watan Janairu.

Sai dai hukumar zaben ta ce ta baiwa matar wadda a halin yanzu ita ce ke wakiltar wannan mazabar a majalisar wakillan kasar takardar shaidar ce saboda umarnin da wata kotu ta ba ta na yin hakan.