Kiran binciken sojoji a Jumhuriyar Nijar

Shugaban majalisar mulkin sojan CSRD, Janar Salou Djibo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban majalisar mulkin sojan CSRD, Janar Salou Djibo

A Jumhuriyar Nijar, wani sabon kawancen kungiyoyin kare hakin dan adam da demokaradiya, da ake kira CADDED, ya yi kira ga gwamnatin Alhaji Mahamadu Isufu ta gudanar da bincike a kan majalisar CSRD ta sojojin da suka tafiyar da mulkin rikon kwarya a kasar.

Kawancen na ganin cewa kamar yadda sojojin suka binciki tsohuwar gwamnatin Tanja Mamadu ,su ma a bincike su dangane da kudade da kadarorin da suka iske na kasa da kuma abin da suka bari a ranar 7 ga watan afrilu da suka mika mulki ga sabbin hukumomi.

Kawancen na CADDED ya yi wannan kiran ne a yau a wajen wani taron manema labarai da ya kira bayan kammala wani taron gaggawa da ya yi nazari , a kan al'amurra da dama da suka shafi makomar kasar ta Nijar.