Wasu karin 'yan gudun hijira sun isa birnin Agadez na Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar Niger, wasu 'yan gudun hijira su akalla dubu da dari biyar ne suka isa birnin Agades, na arewacin kasar a jiya.

'Yan gudun hijirar, wadanda suka tsere wa tashin hankalin da ake yi a Libya, sun hada da 'yan kasar ta Nijar, da 'yan wasu kasashen Afrika da suka hada da Nijeriya da kuma Ghana. Sun bayyana cewa sun ga abubuwa na tayar da hankali a kan hanyarsu, ciki har da gawarwakin wasu 'yan gudun hijirar.

Alkaluman gwamnatin Niger na baya bayan nan dai sun ce akalla mutane dubu casa'in da tara ne suka isa Nijar daga kasashen Libya da Cote d'Ivoire a cikin yan makonnin da suka gabata.

Tuni dai hukumomin kasar ta Niger suka yi kira ga kasashen duniya da su kawo ma su dauki.