Amirka za ta kara hako mai a cikin gida

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya bada sanarwar wasu sabbin matakai na fadada aikin hako mai na cikin gida a Amurka.

A jawabinsa na mako mako da yake yi ta radiyo, ya ce fadada aikin a yankin Alaska da na yankin tekun Mexico, za su taimaka nan gaba, wajen rage dogaro da Amurkar ke yi da sayen mai daga waje.

A baya dai Mr Obama, ya goyi bayan kokarin da ake yi na sauya amfani da makamashi zuwa wanda ba ya gurbata muhalli.

Sai dai a yanzu yana fuskantar korafin jama'a game da tashin farashin man petur.