An kama wasu 'yan asalin Pakistan a Amirka

Wasu 'yan  kungiyar Taliban reshen Pakistan
Image caption Wasu 'yan kungiyar Taliban reshen Pakistan

Hukumomin Amirka na tuhumar wasu mutane shidda, wadanda kusan 'yan gida guda ne, bisa laifin samar da kudi da kayan aiki ga 'yan Kungiyar Taliban reshen Pakistan.

Uku daga cikin mutanen suna da takardun shaidar zama Amirkawa, kuma suna zaune ne a jihar Florida, ciki har da Limamin masallacin birnin Miami, Hafez Khan.

Ragowar mutanen uku kuma suna buya a cikin Pakistan.

Hakazalika mahukuntan Amirkar suna zargin Hafez Khan din da kafa wata madrasa a yankin Swat na Pakistan, inda masu fafutuka ke samun mafaka.

Hukumomi sun ce binciken da ya kai ga kama mutanen uku ya biyo bayan tura wasu kudade ne ta hanyar bankunan da ake shakkunsu zuwa Pakistan din.