Shugaban Asusun IMF na hannun 'yan sanda

Image caption Dominique Strauss-Kahn

Rahotanni sun ce shugaban Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, Dominique Strauss-Kahn, na hannun 'yansanda a jihar New York.

A cewar kafafen yada labarai na Amurka, ana yiwa shugban asusun tambayoyi ne dangane da cin zarafin wata mata a wani otel.

Dominique Strauss-Kahn dai tsohon ministan kudi ne na Faransa, kuma ana masa hangen yuwar kasancewa dan takarar jam'iyyar Socialist a zaben shugaban kasar Faransa wanda za a gudanar nan gaba.

Mintoci kadan kafin jirgin saman da ya shiga daga New York zuwa Paris ya tashi ne dai 'yansanda suka shiga cikin jirgin inda suka wuce da shi domin ya amsa tambayoyin.

Wannan dai bashi ne karo na farko ba da za a kama Mista Strauss-Kahn bisa zargin yin lalalata.

Shekaru uku da suka gabata ma an tilasta masa neman afuwa sakamakon wata dangantaka tsakaninsa da daya daga cikin ma'aikatan Asusun na IMF.