A fadada hare-hare a kan Libya -Richards

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ruwan yaki na kungiyar NATO

Kwamandan rundunonin sojan Birtaniya, Janar Sir David Richards, ya ce ya kamata dakarun NATO su tsananta da kuma fadada hare-haren da suke kaiwa a Libya.

Janar Sir David Richards ya kuma ce idan ba a yi hakan ba, to kuwa Kanar Gaddafi zai ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki.

Ya ce a yanzu kungiyar tsaro ta NATO na bukatar ta kara matsawa Kanar Gaddafi lamba da kuma gwamntinsa ta hanyar amfani da karfin soji domin a nuna masa al'amura sun kara zafi.

Janar Richards da wadansu manyan jami'an soji a kungiyar ta NATO na son su samu goyon bayan mambobin kungiyar wurin kara kaimi a kan hare-haren da za su durkusar da gwamnatin Kanar Gaddafi.

Ya kuma ce duk da cewa hankalin dakarun kungiyar NATO baya kan Kanar Gaddafi, idan yana wani sansanin soji ko cibiyar ba da umarni wanda kungiyar NATO ta kaiwa hari, hakan bai sabawa dokokin yaki ba, kuma dokokin Majalisar Dinkin Duniya sun amince da haka saboda sun ba kungiyar NATO damar amfani da kowacce irin hanya don kare fararen hular Libya.