Yau ake zaben 'yan majalisar dokoki a Agadez

Hakkin mallakar hoto AFP

An bude rumfunan zabe a Jihar Agadez dake Arewacin Jamhuriyar Nijar domin gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki na kasa.

Wakilin BBC ya ce tun da wuri jama'a suka soma fitowa domin su kada kuri'unsu ga wadanda suke son su wakilce su a majalisar.

Tuni har wadansu mazauna babban birnin Jihar suka soma bayyana bukatun su da koke-kokensu ga sabbabin 'yan majalisar dokokin da za a zaba.

Matsalolin da suka addabi jihar dai sun hada da rashin kyawun hanyoyi, da rashin filayen gini ga wadansu talakawa.

'Yan majalisa shida ne dai za a zaba daga cikin jerin 'yan takarar da jam'iyyu ko kawancen jam'iyyu takwas suka gabatar.