An kammala zabe a jihar Agadez ta Nijar

Masu zabe a birnin Agadez Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu zabe a birnin Agadez

A jamhuriyar Niger dazu da magariba ne aka rufe runfunan zabe a fadin jahar Agadez inda kimanin masu jefa kuria dubu dari biyu suka yi zaben 'yan majalisar dokoki na kasa.

Bisa dukan alamu dai, an kammalla ayyukan zaben na yau lafiya ,kuma tuni aka soma kidayar kuri'u a runfunan zabe sama da dari shidda da jahar ta kunsa.

'Yan majalisar dokoki 6 ne dai za a zaba, wadanda kuma su ne za su zama cikamakin 'yan majalisar dokoki 113 da majalisar ta Nijar ta kunsa.

A karshen watan janairu ne dai aka gudanar da zaben 'yan majalisa a duk fadin kasar ta Nijar, amma daga bisani kotun tsarin mulkin kasar ta rusa zaben jahar ta Agadez, bayan da ta gaano cewa takardun shaidar kammala karatu na wata yar takara, na jabu ne.