Shugaban IMF zai gurfana a gaban kotu

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana tuhumar Mr Strauss-Kahn da kokarin aikata fiade

Idan an jima ne ake sa ran shugaban asusun bada lamani na duniya, IMF, Dominique Strauss-Kahn zai gurfana a gaban wata kotu a birnin New York, bisa zargin amfani da karfi wajen neman lalata da wata mai shara a wani otel.

Ana tuhumarsa ne da aikata babban laifin cin zarafi, da kokarin aikata fyade da kuma tsare wata mace ba da son ranta ba. Mataimakin kwamishinan 'yan sanda na New York, Mr Paul Browne ya ce , tun jiya da yamma ake tsare da shi a ofishin 'yan sanda na birnin New York, bayan da aka fito da shi daga wani jirgin sama dake shirin tashi zuwa Faransa.

Lauyan Mr Starus-Kahn dai ya ce zai musanta aikata wannan laifi.