An kashe mutum daya a kan iyakar Syria da Lebanon

Wasu masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu masu zanga-zanga a Syria

Rahotanni daga Lebanon na cewa wani mutum guda ya rasa ransa, yayinda wasu suka jikkata a kan iyakar kasar da Syria, sakamakon wasu harbe harbe.

Kampanin dillancin labarun Faransa na AFP, ya ce an yi harbi da bindiga daga Syria cikin wasu tarin jama'a a kan iyakar Al-Boqayah.

Daruruwan 'yan kasar ta Syria ne ke tsallaka kan iyaka suna shiga Lebanon, sakamakon yadda hukumomin Syriar ke amfani da karfi wajen murkushe zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

A jiya rahotanni sun ce an bindige wasu mutane har lahira a garin Tell Kalakh na kan iyaka.