Ambaliyar ruwa a jihar Louisiana ta Amurka

Ambaliyar ruwa a Louisiana Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kogin Miississippi ya cika ya batse

Ana kwashe dubban jama'a a jihar Louisiana ta Amurka, bayan da a jiya, Asabar, aka bude datsin da aka yi ma kogin Mississippi, wanda ya cika ya batse.

Ana kuma sa ran sake bude irin wannan jerin datsi cikin kwanaki masu zuwa, a karon farko cikin shekaru aru aru.

Wannan ambaliyar ruwa a dalilin bude hanyoyin ruwan, za ta yi sanadiyar lalata dubban gidajen jama'a, da kuma daruruwan eka eka na gonaki.

Jami'ai sun ce wannan ita ce kadai hanyar da za a iya bi a kubutar da wasu yankunan da suka fi yawan jama'a daga malalar da ruwan ke yi; sun kuwa hada da birane, da matatun man petur, da tashoshin bada wutar lantarki, da kuma tashar jiragen ruwa ta New Orleans.