HRW: mutane fiye da dari takwas aka kashe a Najeriya

Wasu matasa na kone-kone a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu matasa na kone-kone a Najeriya

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce mutane fiye da dari takwas ne aka kashe a Najeriya, a kwanaki ukkun da aka kwashe ana tashe-tashen hankula, bayan zaben shugaban kasar na watan Afrilu.

Kungiyar ta ce, ya kamata hukumomin Najeriyar su gudanar da bincike, tare da hukunta masu hannu a lamarin.

Rundunar 'yan sandan Najeriyar ta ce, tuni ta fara gudanar da bincike a kan kashe-kashen, kuma ta kama mutane sama da dari biyar.

Human Rights Watch ta bayyana cewa, ana daukar zabubukan na baya bayan nan a Najeriyar, a matsayin wadanda suka fi sahihanci a tarihin kasar.

To amma kuma suna daga cikin zabubukan da aka fi samun hasarar rayuka.