Moreno ya nemi sammacin kame Gaddafi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luis Moreno Ocampo

Babban mai gabatar da kara na Kotun Hukunta Laifukan yaki ta duniya Moreno Ocampo, ya nemi kotun da ta bada sammacin kame shugaban Libya Kanal Gaddafi da wasu daga cikin manyan jami'ansa.

Mr Ocampo na zargin shugaba Gaddafi da wasu manyan jami'an gwamnatinsa uku cikin harada dansa Saiful Islam, da zargin aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Sai dai gwamnatin Libya ta ce ba za ta saurari kotun ba, saboda kasashe kamar su Amurka basu sa hannu kan yarjejeniyar da ta kaiga kafuwar kotun ba.

Sai dai wasu gwamnatocin Turai na ganin shellar sammacin kamen za ta sa sauran manyan jami'an gwamnatin Libya tserewa daga kasar bisa fargabar sune wadanda za'a kama nan gaba.

Luis Moreno Ocampo yace bincike ya kaisu ga gano cewa Shugaban kasar Libya Mu'ammar Gaddafi ya bayar da odar kashe al'ummar farar hula na kasar, da suka so kalubalantar mulkinsa.

A karkashin dokokin Libya, babban laifi ne wani ya kalubalanci shugabancin Kanar Gaddafi.

Murkushe masu adawa da Gaddafi

Don haka Mr. Ocampo ya ce bincikensu ya kaisu ga gano cewa Kanal Gaddafi ya yi amfani ne da wadansu magoya bayansa da suka hada da dansa Saif Al Islam da kuma babban jami'in hukumar leken asirin kasar Abdullah Al Sanussi, wajen murkushe 'yan adawa.

Yace daga cikin shaidun da ofishin mu ya binciko, harda odar da Mu'ammar Gaddafi da kansa ya bayar.

Binciken ya nuna cewa Gaddafi na amfani ne da wasu magoya bayansa na kusa kusa, wajen murkushe duk wata barazana ga mulkinsa.

Akan haka ne kuma Mr. Ocampo yace sun nemi alkalan kotun da su bada sammacin chafko Kanal Gaddafi da dan nasa da kuma babban jami'in hukumar leken asirin kasar:

"Cikin kasa da watanni uku da suka gabata, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da jawo kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta binciki ta'asar da ake aikatawa a Libya".

A yau kuma mun mika shaidar mu akan haka, inda muka bukaci alkalan kotun ICC din da su bamu takardar sammacin chafko mutanen.

Tun san da masu shigar da kara suka fara wannann binciken a watan Maris din da ya gabata, sun gana da shaidu fiye da hamsin da ta'asar dakarun Kanar Gaddafin ta rutsa dasu.

Sannan kuma sun yi lale akan kundaye fiye da dubu daya da dari biyu, ciki har da hotuna da bidiyo da ke tabbatar da aikata laifuka akan bil adama.