Samuel Wanjiru ya rasu

Marigayi Samuel Wanjiru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Marigayi Samuel Wanjiru

Zakaran gudun yada-kanin-wani na wasannin Olympic, Samuel Wanjiru, ya rasu a gidansa da ke kasar Kenya, yana mai shekaru ashirin da hudu a duniya.

Wani kakakin 'yan sandan kasar ta Kenya ya ce Samuel Wanjiru ya fado ne daga barandar benensa, kuma ya kashe kansa da kansa ne.

To amma kuma wani jami'in 'yan sandan ya ce, hadari ne ya faru bayan tankiyar da ya yi da matarsa, saboda ya kawo wata matar a gidan.

Marigayi Samuel Wanjiru ya sami nasarori a gudun yada-kanin-wanin da aka yi a biranen Chicago da London. Ya kuma sami lambar zinare a wasannin Olympic na Beijing.