Za'a gurfanar da shugaban IMF a gaban kotu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Dominique Strauss Kahn

A yau ake sa ran za'a gurfanar da shugaban asusun bada lamuni na duniya wato IMF, Dominique Strauss Kahn.

A shekaran jiya asabar ne aka kama Mr Strauss Kahn bayan da aka fito da shi daga cikin wani jirgin sama dake gab da shi.

A jiya lahadi ne ya kamata a gurfanar da shi gaban kuliya sai dai an dage ranar zuwa yau litinin.

Hakazalika a daren jiya ne yansanda suka sami sammaci neman shaida ta hanyar gudanar da gwajin kwayar halita wato DNA a'kan tufafin Mr Strauss Kahn.

Bugu da kari lauyoyinsa sun ce ya amince a duba lafiyasa kamar yadda gwamnati ta bukace shi.

Ana dai sa ran Mr Strauss Kahn zai musanta zarge zargen da ake yi masa na yin lalata da wata ma'aikaciya a lokacin da ya kama 'daki a wani babban otel a Manhattan a karshen makon nan.