Masu sa ido sun fara magana akan zaben jihar Agadez

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zabe a Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Niger da maraicen jiya ne aka rufe runfunan zabe a jihar Agadez inda kimanin mutane dubu dari biyu suka kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki na kasa su 6 a jihar.

Bisa dukkan alamu dai an kammala zaben lafiya, kuma tuni aka soma kidayar kuri'u.

Malam Abdoulahy Sidi , wanda ya sai ido akan zaben daga kungiyar ANLC mai yaki da cin hanci ya shaidawa BBC cewa kungiyarsa ta gamsu da zaben duk da cewa an fuskanci wasu kalubale da ya shafi rashin fitilun haskaka wuraren da basu da wutar lantarki.

Zaben 'yan majalisar dokokin dai shi ne zai baiwa majalisar dokokin Niger cikamakin mambobinta da za su tashi 113.