An kashe wani dan Saudiyya a Pakistan

Image caption Birnin karachi na fama da hare-hare

Wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan wata mota ta ofishin jakadancin Saudiyya a garin Karachi na Pakistan, inda suka kashe dan kasar ta Saudiyya.

An kaiwa Hassan Kehqani, wani ma'aikacin jakadanci hari a wata unguwa ta masu hali wacce kuma ke da tsaro sosai.

Harin ya zo ne kwanaki biyu bayan da aka jefa gurneti a ofishin jakadancin, amma babu wanda ya samu rauni.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma al-Qaeda ta yi kaurin suna wajen adawa da gwamnatin Saudiyya.

Kungiyar ta kuma sha alwashin daukar fansa kan kisan da dakarun Amurka suka yiwa shugabanta Osama Bin Laden a Pakistan.

Wani jami'in Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, an kai harin ne kusa da ginin ofishin jakadancin.

"Akalla harsasai shida aka harba lokacin harin," kamar yadda Mataimakin Sufeto Janar na 'yansanda Iqbal Mahmood ya shaidawa manema labarai.

Garin Karachi wanda ke Kudancin kasar ya sha fama da hare-hare a 'yan shekarun nan. Ana fuskantar hare-haren Taliban da kungiyoyin kabilu masu fada da juna kan lamuran siyasa da sauransu.