Shugaban Hukumar IMF ya gurfana a gaban kotu

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dominique Strauss-Kahn

Shugaban Asusun bada lamunin IMF, Dominique Strauss-Kahn, ya gurfana a gaban wata kotu dake birnin New York don fuskantar tuhumar da ake ma shi ta kokarin yiwa wata ma'aikaciyar otel fyade, a ranar Asabar da ta wuce.

Lawyoyinsa sun ce tun karfinsa zai kare kansa daga dukan zarge-zargen da ake ma shi, kuma an jinkirta bayyanar tasa a gaban kotun ne , saboda ana gudanar da wasu gwaje-gwajen kimiyya.

Kafin wannan al'ammari dai, wani bincike jin ra'ayin jamaa da aka gudanar a Faransa, ya nuna cewa Mista Strauss-Kahn, wanda dan jam'iyyar Socialists ne ta masu ra'ayin sauyi, zai iya lashe zaben shugaban kasar Faransa na badi.

A halin da ake ciki kuma, wani zargin ya bullo daga Faransa, game da shugaban na asusun IMF.

Lauyoyi masu wakiltar wata marubuciya a kasar, Tristane Banon, sun ce a yanzu tana duba yiwuwar kai Dominique Strauss-Kahn din kara a kotu, bisa zargin kokarin yin lalata da ita a shekara ta dubu biyu da biyu.