Fararen hula na cikin mummunan hali a Libya

Wasu fararen hula a Libya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu fararen hula a Libya

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kai agaji a Libiya, ya ce halin rayuwar fararen hula na cigaba da tabarbarewa a can, musamman a yankunan yammacin kasar masu tsaunuka.

Jami'in, Panos Moumtzis, wanda bai dade da dawowa daga Libiyar ba, ya ce, ana fama da karancin man petur, da kayayakin abinci da kuma magunguna.

Ya ce an gaya masu cewa, fiye da kashi sittin cikin dari, na ma'aikatan asibitoci 'yan kasashen waje, sun bar Libiyar.

Panos Moumtzis ya ce, ba tare da bata lokaci ba, ya kamata a ba hukumomin agajin majalisar dinkin duniya damar zuwa Libiyar, ta kasa da ta teku.

Ya yi kira da a dakatar da bude wuta, domin a samu a kaiwa fararen hula agaji.