Masana sun yi tsokaci akan shugabanci majalisar Najeriya

Masana kundin tsarin mulkin Najeriya sun ce kundin tsarin mulkin kasar ya ba majalisar datawa ikon ta zauna ta rubuta dokoki wanda zata rika amfani da shi, da wanda zai zayyana yadda zata rika aikinta.

Barista Yahaya Mahamoud masani kan kundin tsarin mulki ya ce duk wani sabon dan majalisa zai iya neman mukamin shugabancin majalisar datawa ko kakakin majalisar wakilai amma ya danganta ne akan idan majalisar ta amince da shi.

Sai dai ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya ba masu rinjaye a majalisar damar aiwatar da dokar da suke so akan haka zasu iya sa dokar da zata ba tsoffafin yan majalisar damar neman shugabanci .

Masanin ya ce hakan ba laifi bane saboda kundin tsarin mulki ya basu damar yin haka.