Shugaban Nijar zai kai ziyara Burkina faso

Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Niger, yau ne ake sa ran shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu zai kai wata ziyarar aiki ta yini guda a kasar Burkina Faso.

Ministan harkokin wajen Nijar, Malam Bazoum Mohamed ya ce abubuwan da shugaban na Niger zai tattauna a'kai tsakaninsa da takwaransa na Burkina Faso, Blaise Compaore, sun hada ne da rikicin da kasar ta Burkina Faso ta fada ciki a 'yan watannin baya, da kuma huldar dake akwai tsakanin kasashen biyu.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaban na Niger, Alhaji Isufu Mahamadu zai kai wata kasa ta waje tun bayan da aka rantsar da shi a ranar 7 ga watan Aprilun da ya gabata.

Hakazalika shugaban kasar nada anniyar zuwa Najeriya domin ya taya shugaba Goodluck Jonathan murna a nasarar da yayi a zaben kasar.