Sarauniyar Ingila na ziyara a Ireland

Sarauniya Elizabeth na ajiye furanni
Image caption Sarauniya Elizabeth na ajiye furanni

Sarauniya Elizabeth ta kai ziyara mai cike da tarihi, a wani wurin tunawa da dimbin 'yan Ireland din da suka yi gwagwarmayar samun 'yancin kai daga Birtaniya.

Sarauniya Elizabeth ta tsaya kafada da kafada da shugabar jamhuriyar Ireland din, Mary McAleese, yayin da suke ajiye furannin a wurin.

Wannan ce ziyarar farko da wani Ba-saraken Birtaniya ya kai kasar ta Ireland, tun bayan da ta sami 'yancin kai shekaru tasa'in da suka wuce.

Gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa, ziyarar Sarauniyar ta bude wani sabon babi a dangantaka tsakaninsu.

To amma masu adawar ganin yankin Arewacin Ireland ya ci gaba da kasancewa wani bangare na Birtaniya, sun yi zanga zanga, kuma tun farko, rundunar sojan Ireland ta kwance wani bam da aka dasa, a wani yanki da aka shirya Sarauniya Elizabeth za ta ziyarta.