Bizimungu zai shafe shekaru 30 a gidan yari

Kotun duniya mai shari'ar mugayen laifufukan da aka aikata a Rwanda, ta yankewa wani tsohon shugaban rundunar sojan kasar, Augustin Bizimungu, hukuncin daurin shekaru 30.

Wannan ya biyo bayan rawar da ya taka ne a kisan kare dangin Rwandan, na shekarar 1994.

Wakilin BBC ya ce, mista Bizimungu ya zauna kurum, ba tare da nuna wata damuwa ba, a lokacin ake yanke masa hukuncin.

Kotun da ke zama a Tanzania, ta kuma sami wani tsohon shugaban runduna ta musamman a Rwandan, Augustin Ndindili-yimana, da aikata laifin kisan kare dangi.

To amma ta sake shi, saboda tuni ya kwashe shekaru goma sha daya a daure.

Kimanin mutane dubu dari takwas ne suka hallaka, a lokacin kisan kare dangin Rwandar.