A Lagos, ana taro kan saka-jari a Afurka

A Nijeriya yau a birnin Lagos, aka bude wani taron yini uku na kasashen Afrika kan batun saka-jari.

'Yan kasuwa, da masana , da kuma masu kampanoni ne ke tattaunawa kan kalubalen da masu saka-jari ke fuskanta a nahiyar, tare da nemo hanyoyin magance hakan.

A Nijeriya dai matsalolin da aka fi kokawa da su, su ne na rashin isasshiyar wutar lantarki, da batun cin hanci da rashawa da kuma wanda ya shafi harkar tsaro.

Tsohon shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a wajen wannan taro.