Shugaba Karzai ya soki matakin Nato

Hamid Karzai
Image caption Shugaba Hamid Karzai ya sha sukar hare-haren Nato kan fararen hula

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, yayi Allah wadai da matakin Nato na bindige mutane 12, kuma wasu tamanin sun sami raunuka, a artabun da suka yi da dakarun tsaro.

Masu zanga-zanga wajejen dubu biyu ne suka bazama a kan titunan birnin Taloqan na lardin Takhar:

Sun fusata ne da harin da sojojin Amirka da na Afghanistan din suka kai jiya da dare, ta sama, inda mutane hudu su ka hallaka, ciki har da mata biyu.

Dakarun da kungiyar tsaron Nato ke jagoranta sun ce, dukan mamatan 'yan gwagwarmaya ne masu dauke da makamai.

Amma mutanen yankin sun karyata hakan.