'Yan Republicans na baya-baya wajen takara da Obama

Image caption Ana fama da rarrabuwar kawuna a jam'iyyar Republican

yayin da 'yan takarar Republican biyu da kuma wasu ke janyewa daga takarar shugaban Amurka a shekarar 2012, har yanzu dai ba'a san 'yan takarar da za su tunkari Shugaba Brack Obama ba. Ko mai ya sa?

Cikin shekara daya da rabi ne dai, Amurka za ta samu sabon shugaban kasa.

Ba kamar kasashen Turai ba, inda ba'a cika damuwa da zaben idan ana saura wata 18 kafin a gudanar ba, za'a iya cewa zancen ba haka yake ba a Amurka a yayin da aka tafka siyasa tsakanin 'yan takarar fidda gwani kafin zaben.

A wannan yanayin da muke ciki ne a shekarun da suka wuce, 'yan takara masu neman kujerar shugaban Amurka ke gudanar da gangamin kamfe da kuma tattara kudin yakin neman zabe, kafin zaben fidda gwani.

A yanzu haka 'yan takara 'yan kalilan ne suka bayyana niyyarsu na tsayawa a zaben shekarar 2012, sauran kamar su Mitt Romney na duba yiwuwar tsayawa takara ko a'a.

Wasu suna ganin siyasar ta Amurka a yanzu shi yafi tafiyar hawainiya a tsawon shekaru 20, bayan da gwamnan Arkansas, wato Bill Clinton ya maye gurbin Shugaba George HW Bush.

A wannan makon ma, wani tsohon gwamna Mike Huckabee, ya ce ba zai tsaya takara ba karkashin inuwar jam'iyyar Republican duk da cewa dai masana na kallonsa a matsayin wani babban dan takara a kasar.

Bayan kwanaki biyu kuma, wani dan kasuwa Donald Trump, ya ce shi ma ba shi da sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa.

Ganin cewa mutane da dama suna kin tsayawa takara wasu kuma sun ki bayyana aniyyarsu, shin wannan alama ce ta tsoro tsakanin 'yan takarar?

A'a ba haka zancen yake ba, In ji Shaun Bowler, wani Farfesa a sashen kimiyyar siyasa dake jami'ar California a Riverside. Ba abun mamaki bane idan mutane sun sauya ra'ayinsu na tsayawa takara.

"A yawancin lokuta da dama mutane na gwada tsayawa takara amma daga baya sai su janye. Tsayawa takarar shugabancin kasa ba karamin aiki bane, dole ne a yi tunani mai zurfi." In ji Shaun Bowler.

Yakin neman zabe

Amma batun dabam yake a wanna karan saboda ba'a san inda za'a soki Mista Obama ba in ji Bowler, kuma a yanzu haka kan jam'iyyar Republican ba a hade yake ba.

Wannan ne kuma ke sa mutane tunanin ko za su tsaya takara ko a'a.

Akwai damar da kuma Mista Obama ya samu, a matsayin shugaba mai ci a yanzu.

Shugabannin Amurka uku ne kawai suka sha kaye akan mulki tun bayan yakin duniya na biyu. Shugabannin su ne Gerald Ford da Jimmy Carter da kuma George HW Bush.

Shugaba mai ci nada suna, kuma yana da kudaden kashewa na kamfe, kuma bai damu da zaben fidda gwani ba a jami'iyyarsa domin yawanci, shi ake tsayarwa.

Wa'adin biyun da Mista Obama zai yi akan mulki na nuni da cewa zai sauka ne a shekarar 2016 idan ya kara cin zabe kenan a badi.

Barack Obama shi ne dan takarar da kowa idonsa ke kai.

Wannan na nufin cewa wasu 'yan takarar jami'iyyar Republican na bata lokacin su ne kawai, in ji S, dake aiki a kamfanin Mitchell Research mai binciken jin ra'ayin jama'a.

Amma ya ce yana ganin za'a samu wani gwarzo a jam'iyyar ta Republican, wanda zai bude muhawara kan tattalin arzikin kasar wanda jama'a da dama suka yi shiru a kai.

"Za'a iya cewa Shugaban kasa zai lashe zabensa, amma idan an jima ana cecekuce kuma da rashin aikin yi da kara kudin iskar gas da man fetur, Obama zai fuskanci gagarumin kalubale."

Kashe shugaban al-Qaeda Osama Bin Laden ya shafi yadda za'a yi takara a Amurka, In ji wani dan siyasar Democrat Peter Fenn. Ya ce kashe Osama ya kwantar da sukar da wasu keyi cewa Mista Obama shugaba ne mai rauni.

"Ina ganin mutane da dama na daukarsa da mahimmaci. Suna ganin irin ci gaban da ya samu a kan kujera." In ji Peter Fenn.

Ra'ayoyin jama'a da aka dauka na nuni da cewa Mike Huckabee zai iya tasiri idan ya tsaya takara, amma dan siyasar ya ce ba shi da niyyar tsayawa, kuma ya ce zai ci gaba da kwangilarsa ne da gidan talbijin na Fox News.