An yiwa Besigye daurin talala a Uganda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban 'yan adawa Besigye

Jam'iyyar adawa a Uganda ta ce an yiwa shugaban jam'iyyar daurin talala.

Yan sanda dai sun hana Mista Besigye zuwa aiki, inda suka zarge shi da shirya zanga-zanga da magoya bayansa, wanda kuma suka ce babban laifi ne.

Mista Besigye ya ce zai umarci lauyoyinsa su kwato masa hakkinsa a gaban kotu.

"Na zabi in dawo gida domin tuntubar lauyoyi na a kan ko me matakin da ka iya hanawa a kama mutum ke nufi, domin ni ban san da wannan batun ba a cikin dokokin mu.

"A da lokacin mulkin kama karya dokar tana nan, kuma a yanzu da alama shugaba Museveni na kokarin sake dawo da wadannan munanan dokokin." In ji Besigye.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce an harbe mutane tara har lahira a zanga-zangar da aka gudanar a 'yan kwanakin nan da aka yi a Uganda.

Karin bayani