Tashin bam ya jikkata wasu a Maiduguri

Rahotanni daga Jihar Bornon Najeriya, sun ce wani bam da ya tashi da safiyar yau a birnin Maiduguri ya jikkata jami'an tsaro biyar dake cikin wata motar sintiri.

Hakan dai ya faru ne bayan da a daren jiya aka shafe kusan sa'a guda, kusa da wani caji ofis, ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad, da aka fi sani da suna, Boko Haram.

A 'yan kwanakin nan dai birnin na Maiduguri na fama da yawaitar hare haren da aka shafe kusan fiye da watanni goma ana kai wa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.