An ba da belin tsohon shugaban Asusun IMF

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Za a ci gaba da jin kara

Kotu ta da belin tsohon shugaban Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, Mr Dominique Strauss-Kahn, wanda aka gurfanar a gaban kotun bisa tuhumar kokarin yin fyade a kan wata ma'aikacin otal a birnin New York.

Mai Shari'ar a Kotun Koli ta jihar New Yrok ta Amurka, Michael Obus, ya yanka kudin belin dala milyan daya, ya kuma ba da umurnin a yi wa Mr Strauss-Kahn din daurin talala, tare da daura wata na'urar lataroni a kafarsa, wadda za ta sanya a san duk inda ya nufa.

Tun ranar Litinin ne dai ake tsare da Wata Kotu a new York ta zargi tsohon shugaban Hukumar lamuni ta Duniya IMF, Dominique Strauss Kahn, bisa kokarin kokarin fyade da a kan ma'aikaciyar otal din.

Mr Strauss Kahn - wanda ya musanta zargin.

Ya yi murabus daga mukaminsa a yau, sannan ya mika pasfo dinsa.