Shugaban Obama ya yi jawabi a kan Gabas ta Tsakiya

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ya nemi a kafa kasar Falasdinawa

Shugaban Amurka Barack Obama, ya bayyana wasu sabbin manufofinsa kan yankin gabas ta Tsakiya bayan guguwar sauyin da ta taso a yankin watannin da suka wuce. Ya yi magana kan yadda mutane suka tashi tsaye a yankin, suka kawo sauyi cikin ruwan sanyi.

Ya ce Amurka na bayansu, kuma burinta shi ne a samu sauyi ta fuskar siyasa da tattalin arziki wanda zai dace da bukatar gama-garin mutane.

Sai dai ya yi gargadin cewa a wasu kasashen bukatar neman sauyin ta hadu da gana azaba daga jami'an tsaro, ba kuma za a amince da haka ba.

Shugaba Obama ya shafe lokaci mai tsawo yana bayani kan rikicin Isra'ila da Palasdinawa, tare da yin kira kan kafa kasar Palasdinu kan iyakokin 1967 kafin yaki, ta hanyar abinda ya kira musayar yankuna cikin ruwan sanyi.

A cewar masu lura da al'amura, kalaman na nuna goyon baya ga bukatar Palasdinawa - da kuma sauyi a manufar Amurka.

Mr Obama ya kuma yi kira ga Isra'ila, yana mai cewa burin Yahudawa na kafa kasar da ke bin dimokuradiyya ba zai cika ba ta hanyar mamaya.

Yac e wajibi ne a tattauna kan muhimman abubuwa a rikicin, kuma abin a bayyane yake, kasar Palasdinu da kuma ta Isra'ila mai cikakken tsaro.