Tankokin yakin Syria sun kai hari Al-Aridha

Sojin Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ji fashe-fashe da ganin hayaki

Rahotanni na nuna cewa tankokin yakin Syria sun kai hari kan garin Al-Aridha dake kan iyakar kasar.

Wani da ya ga abinda ya faru, ya shaidawa BBC cewa yaji fashewar wani abu kuma ya ga hayaki a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce wani mazaunin wani garin na kan iyar kasar da Lebanon, Tel Kalakh, ya shaida musu cewa dakarun Syria sun fara janyewa bayan da suka yi wa garin kawanya ta kwanaki hudu.

Wani mai fafutuka ya ce akalla mutane 27 da aka kashe a yankin, amma babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar.

Wakilin BBC ya ce yawancin mazauna yankin sun yi kaura zuwa Lebanon, a 'yan kwanakin nan domin neman mafaka.