Kungiyar Tarayyar Afrika ta kira taro kan Libya

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika, Jean Ping Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika, Jean Ping

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta kira wani taron gaggawa da za'a yi ranar Laraba mai zuwa domin tattaunawa a kan rikicin kasar Libya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce shugabannin kasashenn kungiyar za su tattauna akan rikicin Libya da kuma sauran rikice rikicen dake faruwa a nahiyar.

Shugabannin Afirka dai na sake dora ayar tambaya ne akan matakin soji na kasashen duniya akan shugaban kasar Libya Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Wannan sanarwar dai ta biyo bayan amincewar da Senegal ta yi da gwamnatin rikon kwarya ta 'yan tawayen dake Bengazi.