An gana tsakanin Obama da Netanyahu

Shugaba Obama ya gana da Praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Washington, kwana guda bayan kaddamar da sabon tsarin Amurka a yankin Gabas ta tsakiya.

Shugaba Obama ya ce sun tattauna game da batun samar da zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Palasdinawa, sun kuma tattauna sosai game da ka'idojin da ya zayyana a jiya, na samar da Kasar Palasdinu a gefen Kasar Yahudawa.

A jiya ne shugaba Obama ya bayyana cewa yarjejeniyar kafa kasashe biyu , ta Isra'ila da ta Palasdinawa, za a yi la'akari ne da kan iyakokin da ake da su a 1967.

Ita dai Isra'ilar na adawa da hakan.